DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar tarayyar Turai za ta tallafa ma gwamnatin Nijeriya da Yuro miliyan 45 don inganta fasahar zamani

-

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta sun kaddamar da sabon mataki na hanzarta sauyin fasahar dijital a Nijeriya, yayin taron kwamitin kula da cibiyar sauyin fasaha da aka gudanar a Kano, kana aka bude Women Venture Studio Innovation Hub.

A cikin shirin, EU za ta bayar da karin tallafin Yuro miliyan 45 ga shirin 3MTT na gwamnatin tarayya, wanda ke da nufin horas da ‘yan Nijeriya miliyan uku a fannoni na zamani kamar AI, tsaron yanar gizo da kirkirar manhajojin komfuta.

Google search engine

Shugabar sashen Green and Digital Economy na EU, Inga Stefanowicz, ta ce manufar ita ce tabbatar da cewa cigaban fasaha ya kasance na kasa baki daya, inda ta jaddada cewa nan da 2025 za a fadada horo da bunkasa fasahar zamani a dukan sassan Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun yi nadamar yekuwar a ba Yilwatda shugabancin APC – Kungiyar magoya bayan jam’iyyar na Arewa ta tsakiya

Kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta bayyana nadamarta bayan ta dage kai da fata sai an naɗa dan yankin...

Zargin El-Rufa’i na biyan ‘yan bindiga Naira biliyan daya ba gaskiya ba ne – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin da tsohon gwamna jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi a Channels TV cewa gwamnatin Uba Sani ta biya ’yan bindiga...

Mafi Shahara