Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan makarantu firamare, sakandare da manyan makarantu ciki har da na masu zaman kansu sakamakon matsalar tsaro.
Rufe makarantun ya biyo bayan munanan hare-hare da aka kai kwanakin nan ciki har da sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.
Haka kuma ‘yan bindiga sun halaka ‘yan sanda biyar a kauyen Sabon Sara a ƙaramar hukumar Darazo ta jihar kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Bauchin ta tabbatar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Ilimi ta jihar Bauchi Jalaludeen Usman ya fitar, gwamnati ta ce rufe makarantun ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro tare da la’akari da tsaron dalibai da malamai.



