Gwamnatin jihar Katsina ta bai wa makarantun firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo damar ci gaba da karatu
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar, ta ce anyi haka ne domin ba da damar zana jarabawar zangon karatu na farko.
Sanarwar ta ce duk da haka dukkannin makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai bayan wani sabon umarni bisa matakan da Gwamnatin jihar Katsina ta dauka don ƙara tsaurara tsaro da kare rayukan ɗalibai da malamai a fadin jihar.
Ma’aikatar ta umurci shugabannin makarantun je-ka-ka dawo da sauran masu ruwa da tsaki su kiyaye tsari da bin dokoki tare da kira ga iyaye su ba ’ya’yansu cikakken goyon baya.



