Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a Nigeria ta yi gargadin cewa yawaitar sace dalibai a makarantun arewa na iya karya ilimi, tare da jefa rayuwar yara cikin mummunar makoma.
A wata hirar da ya yi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, daraktan Amnesty a Nijeriya Isa Sanusi ya ce tsananin tsoro da fargabar sace dalibai na hana su zuwa makaranta, lamarin da ke kara dagula fannin ilimi a yankin.
Sanusi ya bayyana cewa iyayen da ke fama da talauci musamman a karkara na fama wajen tura yaransu makaranta, a yayin da rashin tsaro da sace-sacen yara zai kara hana su yarda da aika ’ya’yansu makaranta.
Ya ce tsoron sace wa kaÉ—ai zai hana dubban yara samun ilimi a arewacin Nijeriya wanda a yanzu yaran da ba sa zuwa makaranta sun haura miliyan 12.



