DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Fashewar tankar man fetur ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dama a jihar Neja

-

Fashewar wata tankar man fetur a cikin gidan mai a Tungan Bunu, karamar hukumar Rijau da ke jihar Neja ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dukiyoyi masu tarin yawa a daren Litinin.

Lamarin ya haifar da firgici a yankin, inda mutane suka yi ta gudun ceton rai.

Google search engine

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa wata majiya ta shaida mata cewa tankar ta iso ne domin sauke mai sai kawai ta kama da wuta, wacce ta fantsama zuwa gidajen dake kusa da su.

Rahoton ya kara da cewa wata tanka ta daban dauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya rufe hanyar gaba É—aya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa tankar dai ta fito daga Legas zuwa Gombe ne, inda ta kife bayan tankin ya balle daga jikin kan motar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara