Wadanda sukai garkuwa da mata 13 da aka sace a jihar Borno sun nemi kudin fansa Naira miliyan 10 domin sakin su.
Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa ‘yan ta’adda ne suka sace matan manoman a ranar Asabar.
Wani ɗan uwa ga ɗaya daga cikin wadanda aka sace ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira ta ne bayan sun saki wata matashiya da ke shayarwa, ya ce an sake ta sannan aka kwace wayarta, aka ba ta sabon layin waya domin ta saka a gida sannan kuka kira suka bayyana bukatarsu.
Ya bayyana cewa al’ummar yankin ba su da karfin biyan wannan kudin, domin yawancinsu manoma ne kuma suna fama da rayuwa.



