Tsohon mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya ce yana fatan shugaban Nijeriya ba zai sake neman kujerar shugabancin ƙasa a 2027 ba.
Ya bayyana hakane a gidan talabijin na Channels, inda ya ce Shugaba Tinubu bai nuna ƙwazo yadda ake buƙata ba wajen gyara kasar, duk da cika burinsa na zama shugaban Nijeriya.
A yayin tattaunawar Dr. Baba-Ahmed ya jaddada cewa tun bayan barinsa gwamnatin Tinubu, ya kan faɗi cewa shugaban ƙasar bai kamata ya sake tsayawa takara ba domin yanzu ya cimma burinsa ba tare da gudanar da mulki yadda ake tsammani ba.
Baba-Ahmed ya ce abin da aka san Tinubu da shi a baya na basira da himma babu alamun irin wannan jajircewar wajen gyaran ƙasa a halin yanzu.



