An bukaci majalisar dokokin Amurka ta matsa wa gwamnatin Nijeriya lamba wajen cire dokar shari’a a jihohin Arewa 12 daga kundin tsarin mulki, tare da rusa hukumomin Hisbah.
Yayin wani taron hadin gwiwa na majalisar wakilan Amurka, mai bayar da shawara a majalisar huldar kasashe, Dr. Ebenezer Obadare, ya zargi cewa kungiyoyi masu haddasa tashin hankali na amfani da tsarin shari’a da hukumomin Hisbah wajen yada akidar tsatsauran ra’ayi, tilasta wa mutane sauya addini, tare da gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar hukunci ba.
Dr. Obadare ya kuma bayar da shawarar yin aiki tare da sojojin Nijeriya don kawo karshen ayyukan ta’addanci a fadin kasar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.



