Majalisar dokokin Nijeriya ta bukaci gwamnatin ƙasar ta bayyana sunayen mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Wannan kira daga majalisar dattawa da ta wakilai, ya zo a daidai lokacin da gwamnati ta bayyana cewa ta fara daukar matakai don magance ta’azzarar matsalar a sassa daban daban na kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A hannu guda, majalisar dattawa ta kuma bukaci a rika zartarwa da masu garkuwa da mutane hukuncin kisa, da kuma duk wanda ke daukar nauyinsu, ko yake taimaka musu da bayanai, yayin da ‘yan majalisar ke tattaunawa kan gyaran dokar hana ta’addanci ta shekarar 2022.



