Jaridar Punch ta rawaito cewa wani jirgin saman yaƙi na rundunar sojin saman Nijeriya (NAF) ya yi hatsari a kusa da kauyen Karabonde da ke ƙaramar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda matuka biyu suka tsira daga cikin jirgin kafin ya kama da wuta.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa jirgin ya tashi ne daga sansanin sojin sama na Kainji, kuma al’ummar yankin sun ce abin ya faru ne misalin ƙarfe 4:10 na yamma, inda aka ga wutar da ta tashi daga wurin da jirgin ya fāɗi.



