Tsohon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina nada ’yan siyasa marasa kwarewa da mutanen da ba su da cancanta domin shugabantar jami’o’in Najeriya.
Jega ya gargadi cewa irin waɗannan nade-naden siyasa suna lalata ingancin jami’o’in tare da raunana tsarin gudanarwarsu.
Jaridar Daily Trust ta ambato shi yana cewa ana bukatar shugabannin da suka dace, masu hangen nesa da kwarewa, ba masu neman ramko ko lada a siyasa ba.
Ya ce tsoma bakin siyasa wajen nada Vice Chancellors, shugabannin gudanarwa, da sauran manyan mukamai ya janyo durkushewar gudanarwa da tabarbarewar ingancin ilimi.
Ya jaddada bukatar tsarin zabe bisa cancanta da gaskiya, domin samun shugabannin da suka fi dacewa. Ya kuma gargadi cewa muddin ba a kawar da tsoma bakin siyasa ba, Najeriya za ta ci gaba da fitar da daliban da ba su da isasshen kwarewa ga ci gaban kasa.
Taron, wanda aka shirya don tunawa da marigayi Prof. Abdullahi Mahadi, ya haɗa manyan malamai da sauran masana a fannin ilimin jami’a a kasar.



