DCL Hausa Radio
Kaitsaye

NSA Ribadu ya gana da tawagar Majalisar Dokokin Amurka a Abuja

-

Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya karɓi wata tawagar ‘yan majalisar dokokin Amurka a Abuja, domin ci gaba da tattaunawa kan al’amuran tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin sakon da ya wallafa a X, Ribadu ya ce ziyarar ta biyo bayan ganawarsu ta baya a Washington D.C., wadda ta mayar da hankali kan manyan batutuwan haɗin gwiwar tsaro.

Google search engine

Tawagar ta ƙunshi ‘yan majalisa kamar Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore, tare da halartar jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills. Ribadu ya ce hakan na nuna muhimmancin da ƙasashen biyu ke bai wa haɗin gwiwar tsaro.

A cewar NSA ɗin, tattaunawar ta ta fi karkata kan yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zaman lafiya a yankin, da hanyoyin inganta alaƙar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Ziyarar ta zo ne a lokacin da ake takaddama kan batutuwan diflomasiyya, musamman bayan matakin gwamnatin Amurka na mayar da Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da take ’yancin addini, matakin da Najeriya ta musanta.

A baya-bayan nan, Ribadu ya gana da Sakataren Yaƙin Amurka Pete Hegseth, sannan Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa US–Nigeria Joint Working Group domin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An kaddamar da kafar yaɗa labarai ta Hausa don mata zalla a Nijeriya

An kaddamar da Mata Media, kafar yaɗa labarai ta farko a Nijeriya da aka ware musamman domin mata, wacce ke aikin shirya labarai na abubuwan...

Ku daina nada baragurbin ‘yan siyasa a shugabacin Jami’o’i – Jega ga Tinubu

Tsohon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina nada ’yan siyasa marasa kwarewa da mutanen...

Mafi Shahara