Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana cewa gaggawar daukar matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ta hana afkuwar babbar barazanar tsaro ga Najeriya.
Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce idan juyin mulkin ya yi nasara, zai ba wa ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin da ke aiki a yankin Sahel damar kara tayar da hankula a Najeriya, musamman ganin cewa wasu sassan Benin sun riga sun cika da gungun masu bore.
Jaridar Punch ta ambato shi na cewa rushewar tsarin mulki a Benin zai iya shafar yankunan kan iyaka na Najeriya kai tsaye.
Gwamnonin sun jinjinawa Sojojin Najeriya bisa saurin mayar da martani da ya taimaka wajen dawo da daidaito a Benin, tare da jaddada cewa barazanar tsaro ga manyan biranen Benin kamar Porto Novo, Cotonou ko Parakou na da tasiri kai tsaye ga Najeriya.



