Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi, ya soki yadda shugabancin siyasa a Najeriya, ke rikidewa daga hanyar ci gaba zuwa mallakar dukjya ta hanyar yaki halal yaki haram.
Sanusi ya bayyana haka ne yayin bikin cika shekaru 15 na Enough is Enough (EiE) Nigeria a Lagos, inda ya ce rashin cigaba yana faruwa ne saboda shugabanni na fifita kansu da masoyansu fiye da bukatun al’umma.
Tsohon gwamnan Bankin Najeriya (CBN) ya yi kira ga matasa su kalubalanci tsarin da ke kawo rikici na kabilanci, addini, da son kai, su hada kai wajen gina Najeriya mai manufa.
Jaridar Daily Trust ta ambato shi ya na jaddada cewa kasar mallakar kowa ce, ba gwamnati ba, kuma kowa na da hakkin bayar da gudummawarsa wajen ci gaban ta wajen ginuwarta.



