DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Obasanjo ya ziyarci fadar shugaban kasa a karin farko tun bayan rantsar da Tinubu

-

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock a ranar Juma’a, karo na farko tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau mulki, abin da ya ja hankalin jama’a ganin yadda ya dade bai halarci fadar ba.

Obasanjo, wanda ya sha sukar gwamnatin Tinubu, ya halarci taron Service of Nine Lessons and Carols na 2025 da Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya.

Google search engine

A taron, ya tuna da lokutan da Nijeriya ke da cikakken tasiri a Afirka, inda ya ce tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter kan sanar da Nijeriya duk wani mataki da Amurka za ta dauka a Afirka.

Kodayake bai yi tsokaci kai tsaye kan rikicin kalaman Amurka da Nijeriya ba, kasancewar Obasanjo a Aso Rock tare da manyan baki irinsu Janar Yakubu Gowon ya kara ɗaga darajar taron, tare da sake bude tattaunawa kan matsayar Nijeriya a idon duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya za ta yi zaman gaggawa kan jadawalin zaben 2027

Majalisar Wakilan Nijeriya za ta koma zama ranar Talata, 17 ga Fabrairu, domin tattauna batutuwan zabe da suka taso bayan sanar da jadawalin zaben 2027...

Kotu ta sahale a binciko takardun karatun Ministan cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar binciken ingancin takardar shaidar sakandare ta Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo. Mai shari’a Binta Nyako...

Mafi Shahara