Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike (autopsy) kan gawar marigayi mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, domin gano ainihin musabbabin mutuwarsa.
Gwamna Diri ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da tsohon Shugaban Nijeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya kai masa ziyarar ta’aziyya a fadar gwamnati da ke Yenagoa.
Diri ya ce umarnin ya zama dole ne sakamakon jita-jita da ke yawo a kafafen sada zumunta game da mutuwar mataimakin gwamnan kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A nasa bangaren, Jonathan ya bayyana mutuwar Ewhrudjakpo a matsayin babban rashi ga al’ummar Bayelsa, yana mai cewa marigayin ya kasance mutum mai himma da aminci, wanda ya wakilci gwamnan jihar a shirye-shiryen Gidauniyar Jonathan, ciki har da taron Democracy Dialogue da aka gudanar a Benin, Jihar Edo.



