DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotun ƙoli ta tabbatar da ikon shugaban ƙasa na ayyana dokar ta-baci

-

Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar da ikon Shugaban Kasa na ayyana dokar ta-baci a kowace jiha domin hana tabarbarewar doka da oda.

A hukuncin da ya samu rinjayen kaso 6–1, kotun ta ce shugaban kasa na da ikon dakatar da zababbun shugabanni a lokacin dokar ta-baci, amma dole ne hakan ya kasance na dan wani lokaci ne kawai.

Google search engine

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Mai shari’a Mohammed Idris ya ce Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki ya ba shugaban kasa damar daukar matakai na musamman domin dawo da zaman lafiya, kodayake bai fayyace irin matakan ba.

Hukuncin ya shafi karar da Jihar Adamawa da wasu jihohin PDP 10 suka shigar, suna kalubalantar dokar ta-baci da Shugaba Tinubu ya ayyana a Jihar Rivers, inda aka dakatar da gwamna da sauran zababbun jami’ai na tsawon watanni shida, inda Kotun ta yi watsi da karar.

Sai dai Mai shari’a Obande Ogbuinya na da sabanin ra’ayi, yana cewa ko da shugaban kasa na iya ayyana dokar ta-baci, ba shi da ikon dakatar da zababbun shugabanni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Idan rikicin PDP ya ki ci, ya ki cinyewa za mu shiga kawance in ji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa dole na iya sanyawa jam’iyyar ta shiga kawance da wasu jam’iyyu idan ƙoƙarin da ake...

‘Yan sandan Nijeriya sun sanar da dawo da aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta sake fara aiwatar da dokar lasisin gilashin mota mai duhu (Tinted Glass Permit), duk da...

Mafi Shahara