Mambobin ƙungiyar kwadago ta kasa NLC sun fara taruwa a hedikwatar NLC da ke Abuja domin gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya kan ƙaruwar matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Daga cikin manyan shugabannin da suka halarci taron akwai shugaban NLC, Joe Ajaero, tare da abokan hulɗa daga ƙungiyoyin farar hula.
Haka kuma, Omoyele Sowore da mambobin ƙungiyarsa ta Revolution Now Movement na daga cikin fitattun mutane da aka gani a wurin.
Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami’an tsaro a yankin, ciki har da ’yan sanda, Civil Defence, da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) domin tabbatar da tsaro.
Tun da farko, Ajaero ya jaddada cewa ba za su fasa zanga-zangar ba, yana mai cewa manufarta ita ce ja hankalin gwamnati kan mummunan tasirin rashin tsaro ga rayuwar al’umma da tattalin arzikin ƙasa.



