Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kwantar wa ’yan Najeriya hankali kan sabbin dokokin haraji da za a fara aiwatarwa a 2026, yana mai cewa za su amfanar da talakawa, masu ƙaramin albashi da ƙananan ’yan kasuwa.
Tinubu ya ce dokokin ba za su shafi abinci, magunguna, ilimi, noma da sufuri daga ba, tare da rage nauyin haraji ga ’yan kasuwa, yana ƙara da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Jaridar Punch ta ruwaito saƙon shugaban ƙasar ya fito ne ta hannun Shugaban Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS), Zaccheus Adedeji, inda Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka sun zama wajibi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.



