Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da nadin jakadu 64 da Shugaba Tinubu ya miƙa mata, ciki har da tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan kafafen sada zumunta, Reno Omokri.
Tabbatarwar ta biyo bayan gabatar da rahoton Kwamitin Majalisar kan Harkokin Waje, wanda shugaban kwamitin Sanata Sani Bello ya ce an tantance dukkan sunayen tare da gano cewa sun cancanta, ba tare da wani ƙorafi ko koke a kansu ba.
Daga cikin waɗanda aka amince da su akwai tsohon Ministan Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau, tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, tsofaffin gwamnonin Enugu da Abia, Ifeanyi Ugwuanyi da Okezie Ikpeazu, da kuma tsohuwar Sanata, Grace Bent. Jimillar sun haɗa da jakadu 34 na aikin ƙwararru da 30 na siyasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya taya sabbin jakadun murna tare da buƙatar su wakilci Nijeriya da mutunci a inda za a tura su, yana mai jaddada cewa babu wani ƙorafi da majalisar ta karɓa kan nadin, duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.



