Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya kafa kwamitin wucin-gadi mai mambobi bakwai domin binciken zargin sabani tsakanin kudirin dokokin haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su da kuma nau’ukan da aka rattaba hannu a kansu tare da wallafawa a jaridar gwamnati.
Hon. Muktar Aliyu Betara zai jagorancin kwamitin, yayin da sauran mambobin suka hada da tsohon Mataimakin Kakaki, Ahmed Idris Wase, da Sada Soli, James Abiodun Faleke, Fred Agbedi, Babajimi Benson da kuma Iduma Igariwey.
Matakin ya biyo bayan korafin da dan majalisa mai wakiltar Sokoto, Hon. Abdulsammad Dasuki (PDP), ya gabatar inda ya ce dokokin harajin da aka wallafa ba su yi daidai da abin da ‘yan majalisa suka tattauna kuma suka amince da shi ba, lamarin da ya bayyana a matsayin karya tsarin majalisa da kundin tsarin mulki.
Dasuki ya ce bayan kwashe kwanaki yana kwatanta rubuce-rubucen dokokin da aka wallafa da bayanan kuri’u da kuma sigar da Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa suka amince da ita, ya gano bambance-bambance masu yawa, yana mai cewa abin da aka wallafa ba shi ne abin da aka zartas ba.



