Wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ogbon-Inu Taiwo Popoola, ya mutu a Jihar Ebonyi yayin da yake halartar taron shugabanci a hedkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abakaliki.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na safiyar Talata, inda marigayin, wanda shi ne jami’in kula da Sashen Leken Asiri na jihar, ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi a tsakiyar taron.
An gaggauta kai shi asibitin ‘yan sanda da ke hedkwatar rundunar a Abakaliki, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa. Binciken farko ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya da ke da alaƙa da hawan jini.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Joshua Ukandu, ya tabbatar da rasuwar, yana mai cewa marigayin bai kasance mara lafiya ba kafin faruwar lamarin, tare da bayyana shi a matsayin jami’i mai jajircewa da kwarewa. An ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Alex Ekwueme da ke Abakaliki.



