Kwamandan rundunar sojin Nijeriya ta Guwards Brigade , Birgediya Janar Adebisi Onasanya, ya gargaɗi ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a Abuja da sauran wurare cewa za su dandana kudarsu a shekarar 2026, domin za a ƙara matsa musu lamba ta fuskar tsaro.
Janar Onasanya ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Asabar, yayin ganawa da manema labarai a Aso Rock.
Ya bayyana cewa shekarar 2025 ta kasance mai matuƙar ƙalubale, sakamakon ƙarin buƙatun tsaurara tsaro fiye da aikin kare shugabanni kaɗai.
A cewarsa, rundunar ta tsabtace yankuna a wurare daban daban a Abuja da wasu sassan jihar Neja, inda aka kama masu laifi, aka kwato makamai, tare wasu ’yan ta’adda,ya ce nasarorin sun samu ne ta hanyar haɗin gwiwa da ’yan sanda, NSCDC, DSS, da kuma goyon bayan sojin ruwa da sojin sama.



