DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jam’iyyar PDP tsagin Turaki ta nemi kotu ta umurci ‘yan sanda su bude sakatariyar jam’iyyar

-

Jam’iyyar PDP bangaren Kabiru Turaki (SAN) ta shigar da ƙara a Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman umarni da zai tilasta wa ’yan sanda su buɗe tare da ficewa daga sakatariyar ƙasa ta jam’iyyar da ke Wadata Plaza.

An rufe sakatariyar ne tun watan Nuwamba bayan rikici tsakanin bangaren Turaki da bangaren da ke goyon bayan Ministan FCT, Nyesom Wike, sakamakon shirya taruka a rana guda, lamarin da ya janyo tsoma bakin ’yan sanda da kulle ginin.

Google search engine

Bangaren Turaki ya ce kullen ya hana shugabancin jam’iyyar gudanar da ayyukanta, inda suke roƙon kotu ta umarci ’yan sanda su cire shingaye tare da hana su sake kulle ofisoshin PDP a Abuja da jihohi 36 har sai an yanke hukunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun saurari kiran da aka ba da umarnin kama ni bayan wani ya yi kutsen wayar Ribadu – El-Rufai

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ya saurari wata tattaunawar waya da ya danganta da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA),...

El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da hannu a yunƙurin sanya Kwankwaso cikin jerin takunkumin Amurka

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya kasancewa a bayan yunƙurin dan Majalisar Dokokin Amurka,...

Mafi Shahara