Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa salo guda ɗaya ne kacal sahihi na sabbin dokokin gyaran haraji da aka rattaba wa hannu, tare da musanta zargin cewa an sauya dokokin bayan Majalisar Tarayya ta amince da su.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana haka a taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar an Abuja.
Ministan ya ce dokokin sun bi dukkan matakan doka a Majalisar Tarayya kafin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba musu hannu, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da su kamar yadda aka tsara. Sai dai ya ce Majalisar Tarayya na duba koken da aka shigar game da zargin bambanci tsakanin abin da aka amince da shi da abin da aka wallafa a mujallar gwamnati.
Rigimar ta biyo bayan korafin dan Majalisar Wakilai Abdussamad Dasuki na Kebbe/Tambuwal, wanda ya ce akwai wasu sashe a dokokin da ba a tattauna ba amma aka saka su. Duk da sukar da wasu ‘yan siyasa suka yi, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, gwamnati ta ce dokokin za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, yayin da shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce jinkirta aiwatarwa na iya jefa Nijeriya cikin matsala.



