DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya za ta rufe shafukan sada zumunta na ‘yan ta’adda

-

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa hukumomin tsaro na Nijeriya na aiki tare da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta domin gano tare da rufe asusun da ‘yan ta’adda da masu laifi ke amfani da su wajen tallata ayyukansu da tara kuɗi.

Babban Daraktan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), Manjo Janar Adamu Laka, ya bayyana hakan ne a taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja, inda ya ce ‘yan ta’adda na amfani da kafafe irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X wajen nuna hare-harensu, baje kayayyakin da suka sace, da sadarwa da magoya bayansu.

Google search engine

Ya ce hukumomin tsaro sun yi tarurruka da dama da wadannan kamfanoni domin magance wallafe-wallafe da asusun da ke barazana ga tsaron ƙasa.

Laka ya ƙara da cewa dabarun ‘yan ta’adda na ci gaba da sauyawa, ciki har da amfani da sunaye na bogi da asusun da ba a tantance ba, amma ya jaddada cewa hukumomin tsaro na ci gaba da daidaita dabarunsu domin tinkarar sabbin barazanar tsaro a Nijeriya.

1 COMMENT

  1. Tatsuniyar Gizo bata wuce ta Qoqi. Idan har Gwamnati da gaske take mine ne zai hana a bibiye su a Kashe na Kashewa a kama na Kamawa. Amma inda wani yau zai ci zarafi Shugaban Kasa to Wallahi na tabbata mutum ko cikin Rami ya Binne kansa sai Hukumar DSS ta kama shi. Amma abin mamaki sai gashi Mutanen da suke daukar Bidiyon kansu suna shelar irin Makaman da suke rikewa da kuma irin Ta’asar da suke yi, amma kuma an gagara Bibiyarsu. Shi yasa mu ‘Yan Kasa muke cewa Gwamnati ba da gaske take yi ba dangane da magance Matsalar Tsaro a Kasar na ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara