DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kananan hukumomi sun bukaci a rika biyan kudadensu kai tsaye daga asusun Gwamnatin Tarayya

-

Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi (NULGE) sun mara wa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu baya kan shirin tilasta biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Tinubu ya yi gargaɗin cewa zai fitar da umarni na shugaban ƙasa idan gwamnonin jihohi suka ƙi bin hukuncin Kotun Ƙoli.

Google search engine

Kotun Ƙoli a ranar 11 ga Yuli, 2024 ta haramta wa jihohi riƙe ko sarrafa kuɗaɗen ƙananan hukumomi, tare da bayyana tsarin kwamitin rikon ƙwarya a matsayin saɓa wa Kundin Tsarin Mulki. Duk da haka, har yanzu ba a aiwatar da hukuncin gaba ɗaya ba.

Binciken The PUNCH ya nuna cewa jihohi sun cigaba da sarrafa Naira tiriliyan 7.43 na kuɗaɗen ƙananan hukumomi daga Yuli 2024 zuwa Disamba 2025, duk da umarnin biyan kuɗaɗen kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da aiwatar dokokin haraji

Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji, tana mai cewa rikice-rikicen da suka...

Babu wasu sauye-sauye a dokokin haraji – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa salo guda ɗaya ne kacal sahihi na sabbin dokokin gyaran haraji da aka rattaba wa hannu, tare da musanta zargin...

Mafi Shahara