Hukumar Tattara Haraji ta Nijeriya (FIRS) ta bayyana cewa lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN) da Hukumar NIMC ke bayarwa ta zama kai tsaye lambar haraji (Tax ID) ga daidaikun ‘yan Nijeriya, a ƙarƙashin sabbin dokokin haraji.
FIRS ta sanar da hakan ne a wani shirin wayar da kai kan sabbin dokokin haraji da ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin, inda ta ce ‘yan kasuwa masu rijista ma ba za su ƙara buƙatar wata lambar haraji ta daban ba, domin lambar rijistar CAC (RC) za ta zama lambar harajinsu.
Hukumar ta ce Dokar Gudanar da Haraji ta Nijeriya (Nigeria Tax Administration Act – NTAA), wadda za ta fara aiki daga Janairu 2026, ta tanadi amfani da Tax ID a wasu mu’amaloli, ciki har da mallakar asusun banki, amma ta jaddada cewa wannan ba sabon tsari ba ne tun daga Dokar Kuɗi ta 2019.
A cewar FIRS, sabon tsarin zai haɗa dukkan lambobin haraji zuwa guda ɗaya, rage maimaituwa, toshe hanyoyin gujewa biyan haraji, tare da inganta gaskiya da adalci a tsarin karɓar haraji a Nijeriya.



