Tsohon Shugaban Matasa na Ƙasa kuma Sakataren Kuɗi na Jam’iyyar PDP, Rt. Hon. Abdullahi Hussaini MaiBasira, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
MaiBasira ya bayyana hakan ne a wata wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 22 ga Disamba, wadda ya aike wa shugaban jam’iyyar PDP na mazabarsa ta Tudun Wada ta Kudu, Karamar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja, inda ya ce murabus ɗin ya fara aiki nan take.
A cikin wasiƙar, MaiBasira ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi ya yi aiki a matakai daban-daban tsawon shekaru, yana mai bayyana shawarar barin PDP a matsayin mai matuƙar wahala. Duk da haka, bai fayyace dalilin murabus ɗin ba, sai dai ya ambaci abin da ya kira “yanayi bayyanannu da matsin lamba na zahiri” a cikin jam’iyyar.
Ficewar tasa na da tasiri a siyasar PDP a Jihar Neja, la’akari da rawar da ya taka a harkokin matasa da tsare-tsaren jam’iyya a matakin jiha da ƙasa.
Ko da yake bai bayyana inda zai dosa ba, majiyoyi daga jam’iyyar na hasashen cewa MaiBasira na iya komawa Jam’iyyar ADC, musamman ganin alaƙarsa da goyon bayan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.



