Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da aiwatar da sabbin dokokin sauya haraji da aka tsara fara aiki a watan Janairu, sakamakon ce-ce-ku-ce kan yadda aka tsara dokokin bayan amincewar Majalisar Tarayya.
Ndume ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, inda ya ja hankalin gwamnati kan rahotannin da ke nuna cewa an canza wasu sassa na dokokin bayan amincewa da su.
Hakazalika ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya kafa kwamitin bincike na musamman domin tantance gaskiyar dokokin da kuma gano sahihancin zargin canje-canjen kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sanatan ya gargadi cewa fara aiwatar da dokokin ba tare da warware zarge-zargen ba zai iya haifar da matsalar inganci da rage amincewar jama’a ga dokokin gwamnati.



