Masu binciken manyan laifuka (Central Crime Branch) a ƙasar Indiya sun cafke wata ’yar Nijeriya mai shekara 29, Olajide Esther Iyanuoluwa, bisa zargin safarar hodar iblis da ta ɓoye gram 121 a cikin biredi.
Jaridar Punch ta ruwaito, an kama Olajide ne a Bengaluru bayan samun bayanan sirri, inda aka ƙiyasta darajar hodar iblis ɗin da aka ƙwato da kusan rupee crore 1.2. An ce ta shigo Indiya da takardar ɗaliba amma ba ta taɓa yin rajista a wata makaranta ba.
’Yan sanda sun ce ta rika sauya matsuguni a Mumbai da kewaye, tana karɓar hodar iblis daga wani mutum da kanta tana kai ma wani ɗan Nijeriya a Bengaluru domin kauce wa shakku.
An gano hodar iblis ɗin ne bayan bincike, inda aka samu ta ɓoye a cikin burodin da aka hurhuda rami aka cika da ƙwayoyin. Daga bisani an kama wanda za a miƙa wa kayan, wanda aka ce an kore shi daga Indiya, yayin da bincike ke ci-gaba domin gano sauran masu hannu a safarar.



