Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya ce cin hanci da rashawa na boye albarkar da Allah Ya yi wa Nijeriya tare da hana ƙasar cimma cikakken ci-gabanta.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Laraba yayin saƙon Kirsimetinsa ga ’yan Nijeriya, inda ya yi kira da a haɗa kai wajen yaƙar cin hanci da rashawa domin ƙasar ta samu ƙarfi da wadata. Ya ce cin hanci na daga cikin manyan matsalolin da ke hana albarkar rayuwa da Allah Ya tanadar wa ƙasa.
Ya kuma bukaci ’yan Nijeriya su rungumi ƙimomin da Annabi Isa (AS) ya koyar na soyayya, haske da fata yana mai cewa su ne ginshiƙan ciyar da ƙasa gaba.
Shugaban EFCC ya ƙara da kira ga jama’a su goyi bayan ajandar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa fata da amincewa cewa Nijeriya za ta iya shawo kan ƙalubalen da ke gabanta.



