Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Tarayya ta tura ƙarin rundunonin tsaro na musamman zuwa Maiduguri, Jihar Borno, domin kamo waɗanda suka kai harin bam a masallacin Al-Adum da ke kasuwar Gamboru.
Shettima ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, bayan harin da ya kashe mutane biyar tare da jikkata wasu a lokacin sallar magariba ranar Laraba.
A cewarsa, Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya ba da umarnin ƙara tsaurara matakan tsaro a Borno, yana mai jaddada cewa gwamnati na aiki tare da hukumomin jiha da jami’an tsaro domin kare al’umma da muhimman gine-gine a Arewa maso Gabas.
Shettima ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye ba, yana mai tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa za a hukunta masu hannu a harin bisa doka, tare da jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.



