‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, suna zargin take kundin tsarin mulki da rashin kyakkyawan tafiyar da majalisar.
’Yan majalisar sun sanar da haka ne a Gusau a daren Laraba, 24 ga Disamba, bayan taron haɗin gwiwa, inda suka ce shugabancin majalisar ya mayar da kansa tamkar reshen zartarwa ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal.
Sun bayyana cewa an dakatar da su “ba bisa ƙa’ida ba” kusan shekara biyu, lamarin da ya hana al’ummarsu wakilci, har suka tilasta kafa majalisa ta daban domin kalubalantar abin da suka kira ayyukan ba bisa doka ba.
’Yan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon. Bashar Aliyu Gummi, Hon. Nasiru Abdullahi Maru, Barr. Bashir Abubakar Masama, Hon. Bashir Bello, Hon. Amiru Ahmad Keta da Hon. Muktar Nasir Kaura. Sun kuma nemi Majalisar Ƙasa ta binciki rikicin majalisar Zamfara, tare da zargin PDP da rikice-rikicen cikin gida da gazawar shugabanci.



