Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ce rundunarta ta musamman (STS) ta kama wani fursuna da ya tsere daga gidan gyaran hali da kuma wasu mutane 21 a jihohi daban-daban bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, satar shanu, satar mota, safarar miyagun ƙwayoyi da kwaikwayon jami’an tsaro.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya ce an kai samamen ne bisa sahihan bayanan sirri, inda aka ƙwato bindigogi shida ciki har da AK-47, AK-49 da LAR, tare da harsasai, motoci, babura da sauran kayayyakin laifi.
A cewarsa, daga cikin wadanda aka kama har da Ayo Abiodun, fursunan Kuje da ya tsere, da ake zargi da fashin wani jami’in soja, da kuma wasu mutane da ke da alaƙa da ’yan fashi da masu garkuwa da mutane a Kaduna, Abuja, Lagos, Ogun, Edo da Nasarawa.
Hundeyin ya ƙara da cewa bincike na ci-gaba, kuma za a gurfanar da dukkan waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike, yana mai jaddada kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya.



