Akalla ma’aikatan jinya da ungozoma 16,156 ‘yan Nijeriya sun samu lasisin aiki a kasar Birtaniya tsakanin 2017 zuwa 30 ga Satumba, 2025, a cewar bayanan Hukumar Kula da Jinya da Ungozoma ta Birtaniya (NMC).
Rahoton ya nuna yadda matsalar “japa” ke ƙara kamari, inda ƙwararrun ma’aikatan lafiya ke barin Nijeriya zuwa ƙasashen da ke ba da albashi mai tsoka, damar ci-gaban aiki da kyakkyawan yanayin aiki. Wannan na jefa tsarin kiwon lafiyar Nijeriya cikin barazana, musamman a yankunan karkara.
NMC ta tabbatar da cewa zuwa ƙarshen Satumba 2025, akwai ma’aikatan jinya 16,156 da aka horas a Nijeriya a kundin rijistarta. A watan Maris 2025, adadin ya kai 15,421, ƙaruwa da kashi 4.8 cikin watanni shida. Nijeriya na cikin ƙasashe uku da ke kan gaba wajen tura ma’aikatan jinya zuwa Birtaniya, bayan Philippines da India.
Haka kuma, rahoton jaridar Punch ya ruwaito cewa, kididdigar 2025 ta nuna cewa ma’aikatan lafiya 43,221 ciki har da likitoci, masu jinya, ungozoma da masu gwaje-gwaje sun bar ƙasar tsakanin 2023 da 2024, lamarin da ke ƙara tsananta ƙarancin ma’aikata a tsarin lafiya.



