Sojojin Nijeriya karkashin rundunar hadin gwiwa ta Faruruwa sun samu nasarar kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a kan iyakar jihar Kano da Katsina da safiyar Lahadi.
Mai magana da yawun runduna ta 3 da ke Kano Manjo Zubairu Babatunde, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN cewa an samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a yankunan Daurawa da Kira da ke kan iyakar Katsina da Kano.
A cewar sa, bayan dauki ba dadi da ‘yan bindigar, sojojin sun samu nasarar kubutar da mutumin mai suna Rabi’u Alhaji Halilu, wanda ya samu raunin harbi a kafarsa.
Rundunar dai ta ce tuni aka mika shi asibiti don samun kulawar gaggawa.
Haka kuma ta samu nasarar kwato tarin babura da kuma shanun da ake kyautata zaton na sata ne wadanda ‘yan bindigar suka tsere suka bar su.



