Sojojin rundunar haɗin gwiwa na Joint Task Force sun yi nasarar ceto wani mutum da aka sace tare da kwato wasu shanu da ‘yan bindiga suka kwace, bayan artabu da suka yi da su a iyakar jihohin Kano da Katsina.
Rahotanni daga rundunar sojin sun nuna cewa lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi a yankin Yankwada na jihar Kano, bayan sojoji sun samu bayanan sirri kan motsin wasu ‘yan bindiga da ke shigowa daga yankunan Daurawa da Kira na jihar Katsina zuwa bangaren Kano.
Majiyoyin sojin sun bayyana cewa dakarun sun tare ‘yan bindigar ne a yankin Ungwan Dogo da Ungwan Tudu, inda aka yi musayar wuta mai zafi tsakaninsu.
A yayin artabun, an samu nasarar ceto wani mutum mai suna Rabiu Alhaji Halilu, mai shekaru 38, wanda aka sace,sai dai rahotanni sun ce an harbi Halilu da bindiga a kafa, inda aka gaggauta kai shi asibitin na soji da ke Faruruwa domin samun kulawar likitoci.



