DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Nijeriya za ta kara mayar da hankali kan tsaurara matakan kudi da gyaran haraji a 2026 – Shugaba Tinubu

-

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa shekarar 2026 ta zo da sabon mataki mai karfi na bunkasar tattalin arziki, inda ya ce gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar a 2025 sun fara haifar da sakamako mai kyau.

A cikin sakon sabuwar shekara, Shugaba Tinubu ya ce duk da kalubalen tattalin arzikin duniya, Nijeriya ta samu ci gaban ma’aunin tattalin arziki na GDP sama da kashi 4 cikin 100, saukar hauhawar farashi zuwa kasa da kashi 15, kudin Naira sun fara daidaituwa, da kuma karuwar jarin kasashen waje.

Google search engine

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta kara mayar da hankali kan tsauraran matakan kudi da gyaran haraji a 2026, domin gina tattalin arziki mai dorewa.

Ya bayyana cewa sabon tsarin haraji zai rage nauyin haraji da kudade ga jama’a, tare da samar da kudin shiga da za a yi amfani da su wajen gina hanyoyi, wutar lantarki, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Shugaba Tinubu ya kuma ce kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta samu gagarumar riba, alamar karuwar amincewar masu zuba jari.

A bangaren tsaro da walwalar al’umma, Shugaban ya jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yiwu ba tare da zaman lafiya ba. Ya ce hukumomin tsaro za su kara hadin gwiwa da kasashen duniya domin dakile ta’addanci da ‘yan bindiga. Haka kuma, gwamnatin za ta aiwatar da shirin Renewed Hope Ward Development Programme domin tallafa wa akalla mutane miliyan 10 a fadin kananan hukumomi, ta hanyar noma, kasuwanci da sarrafa albarkatu. Shugaban ya kammala da kiran hadin kai, yana mai cewa gina kasa nauyi ne na kowa da kowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 daga masu tura kudi ta banki da suka kai N10,000

Daga 1 ga watan Janairun, 2026, bankunan Nijeriya za su fara cire harajin N50 kan duk wanda ya tura kudi da ya kai ₦10,000 ko...

KasashenNijar, Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba wa ’yan Amurka takunkumin biza

Kasashen Nijar,Burkina Faso da Mali sun sanar da kakaba takunkumin biza ga ’yan ƙasar Amurka, a matsayin martani ga dokar hana shige da fice da...

Mafi Shahara