Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta sanya 7 ga Janairu domin yanke hukunci kan bukatar beli da Abubakar Malami, tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, ya gabatar bisa zargin safarar kudi.
A halin yanzu, Malami na tsare a gidan gyara hali na Kuje tare da dansa, Abdulaziz Malami, da daya daga cikin matansa, Bashir Asabe, wadanda ke fuskantar shari’a a gaban kotu.
Hukumar EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 a kansu, tana zarginsu da safarar kudade har Naira biliyan 8.7. Dukkaninsu sun musanta zargin lokacin da aka gurfanar da su a ranar 29 ga Disambar 2025.



