DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwankwaso ba shi kadai ya ƙirƙiri Kwankwasiyya ba – Dr Adamu Dangwani

-

Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka assasa tafiyar Kwankwasiyya Dakta Adamu Dangwani ya ƙaryata zargin da ake yi cewa wasu tsoffin abokan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun ci amanar tafiyar Kwankwasiyya.

Ya baiyana cewa waɗanda ke yin irin wannan zargi ba su fahimci ma’anar cin amana ba.

Google search engine

Dr. Dangwani yayin wata tattaunawa da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta intanet a Kano ya jaddada cewa tafiyar Kwankwasiyya ba mallakin mutum ɗaya ba ce tare da cewa ƙungiyar an samar da ita ne tare kuma an ba ta suna ne ta hannun ƙananan ’yan siyasa da masu ilimi ba wai Sanata Kwankwaso kaɗai ya ƙirƙire ta ba.

Ya ce kalmar Kwankwasiyya da kafuwar ƙungiyar tun asali ra’ayi ne na mutane shida, ciki har da Alhaji Salisu Buhari, Farfesa Hafiz Abubakar, wani tsohon minista da aka sani da Borodo, Farfesa Umar Farouk, Alhaji Rabiu Suleiman Bichi da shi kansa.

Ya jaddada cewa siyasa ra’ayi ce kuma sabanin ra’ayi ba cin amana ba ne, sa’annan rabuwa a siyasa abu ne na al’ada kamar yadda hakan ke faruwa ko a cikin iyali.

Dr. Dangwani ya ƙara da cewa hanyoyinsu da Sanata Kwankwaso sun bambanta ne lokacin da tsohon gwamnan Kano ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP ba tare da tuntubar wasu daga cikin makusantansa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tankiya tsakanin Nijer da Benin ta sa kasashen rufe ofisoshin jakadancin juna

Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a...

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane fiye da 30 a jihar Neja

Aƙalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, Borgu LGA a...

Mafi Shahara