Majalisar Dokokin jihar Rivers ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara tare da mataimakiyarsa Ngozi Oduh, bisa zargin aikata manyan laifuka da saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa a zaman majalisar da aka yi ranar Alhamis, 8 ga Janairu, 2026, wanda aka watsa kai tsaye ta gidan talabiji na Channels,wanda Shugaban Majalisa Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban masu rinjaye, Hon. Major Jack, ya karanta takardar zarge-zarge da manyan laifuka da ake yi wa Gwamna Fubara.
‘Yan majalisa 26 ne suka sanya hannu kan takardar, inda suka ce zarge-zargen sun shafi saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
Shugaban majalisar, Amaewhule, ya ce za a miƙa wa Gwamna Fubara takardar sanarwar zarge-zargen cikin kwanaki bakwai masu zuwa, kamar yadda doka ta tanada.



