Kamfanin haraji na KPMG, ya bayyana cewa ya gano manyan kura-kurai, a cikin sabbin dokokin haraji na Nijeriya, duk da burin da gwamnati ke da shi na inganta tattara kuɗaɗen shiga da sauƙaƙa tsarin haraji.
Rahoton KPMG ya fito ne bayan shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokokin a ranar 26 ga Yuni, 2025, inda suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
A wata sanarwa da KPMG ta fitar ta ce duk da cewa dokokin na da damar ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati idan aka aiwatar da su yadda ya kamata, akwai buƙatar gyara cikin gaggawa domin cimma manufar gyaran harajin.



