Majalisar Dokokin jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga jam’iyyar NNPP, tana mai cewa rikicin shugabanci da shari’o’in kotu da ke addabar jam’iyyar na iya jefa kujerarsa cikin barazana.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar, Hon. Lawan Hussaini, ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis, inda ya ce ci gaba da zama a NNPP ya zama hadari ba ga gwamna kaɗai ba, har da sauran zababbun jami’an gwamnati a jihar.
Daily Trust ta rawaito Hussaini, na cewa NNPP na fama da rarrabuwar kawuna a shugabanci da kuma tarin shari’o’in kotu, lamarin da ke janyo rashin tabbas kan sahihancin tsarin jam’iyyar da tsayar da ’yan takara a zabuka masu zuwa.



