Kasar Benin Republic za ta gudanar da zaɓukan ’yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi a ranar Lahadi, wata guda bayan wani yunkurin juyin mulki da ya girgiza ƙasar, zaɓen da ake ganin zai yi tasiri kan zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya yi a watan Afrilu.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna cewa jam’iyyun da ke ƙarƙashin hadakar shugaban ƙasa, Patrice Talon, na dab da ƙarfafa ikonsu, musamman ganin yadda babbar jam’iyyar adawa ta Democrats ba za ta shiga zaɓukan ƙananan hukumomi ba, kuma an hana ta shiga zaɓen shugaban ƙasa saboda rashin cika sharudda.
A halin yanzu, jam’iyyar Democrats za ta shiga zaɓen majalisa, amma ana fargabar za ta rasa kujeru da dama, kasancewar hadakar jam’iyyar Talon na rike da kujeru 81 cikin 109 na majalisar ƙasar.
Zaɓen na zuwa ne a daidai lokacin da Benin ke fuskantar matsin lamba bayan yunkurin juyin mulki na ranar 7 ga Disamba, wanda sojoji suka dakile cikin sa’o’i tare da taimakon Nijeriya da Faransa.



