Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party LP,Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa Peter Obi zai samu tarba a LP idan har bai samu tikitin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ba a zaɓen 2027.
Datti ya bayyana hakan ne a ranar Jumma’a yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin Channels, inda ya ce ya fi dacewa Obi ya dawo jam’iyyar da suka tsaya takara tare a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Sai dai Datti ya ce yana alfahari da abin da suka yi tare da Obi a baya, yana mai jaddada cewa har yanzu shi jagoran LP ne kuma bai fice daga jam’iyyar ba, sabanin rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta.



