Alamu na nuna cewa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga tsakani a rikicin siyasa da ke gudana tsakanin Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Wata babbar majiyar fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya kira Wike domin tattaunawa kan rikicin, inda ake sa ran za a yi ganawar a wajen Nijeriya.
Rahotanni sun kuma ce Gwamna Fubara ya bar Nijeriya a ranar Alhamis da nufin ganawa da Tinubu a kasar Faransa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan majalisar dokokin Jihar Rivers, da ake dangantawa da Wike, suka kaddamar da sabon yunkurin tsige Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bisa zargin aikata manyan laifuka.
Majiyar ta shaida ma jaridar Punch cewa shugaba Tinubu ba zai lamunci rikicin ya kara dagulewa ba, musamman ganin barazanar tabarbarewar tsaro da tasirinsa ga arzikin kasa. Ta ce Tinubu na ganin matakin tsige Fubara a wannan lokaci na iya haddasa rikici a yankin Neja Delta, lamarin da ya sa ya dauki matakin shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya.



