Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da sabon alawus na farfesoshi wanda zai ba su damar karɓar ƙarin kuɗi sama da ₦140,000 a kowane wata, tare da ƙarin albashi kashi 40 cikin 100 ga dukkan malaman jami’o’in gwamnati.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin hira da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV, bayan cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) bayan shafe shekaru 16 ana takaddama.
A cewar Alausa, yarjejeniyar ta 2025 ta kawo ƙarshen rikicin sake duba yarjejeniyar 2009, inda aka tsara alawus na ilimi guda tara (9) cikin tsari mai kyau, ciki har da sabon tsarin alawus na Farfesa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi.
Ministan ya tabbatar da cewa gwamnati ta riga ta fara aiwatar da yarjejeniyar, yana mai cewa an fitar da dukkanin takardun doka da ke goyon bayan walwalar malamai, kuma an tanadi kuɗaɗen da za su tabbatar da aiwatar da ƙarin albashin kashi 40% da sabbin alawus-alawus ba tare da tsaiko ba.



