Gwamnatin Nijeriya ta umurci dukkan bankuna da kamfanonin fintech su fara karɓa da tura harajin VAT kashi 7.5 cikin 100 kan wasu ayyukan banki na zamani daga Litinin, 19 ga Janairu, 2026.
Harajin zai shafi kuɗaɗen hidimar banki irin su cajin tura kuɗi ta waya, USSD, da kuɗin fitar da kati, amma ba zai shafi kuɗin da ake turawa ba, sai cajin hidimar kawai. Misali, idan cajin tura kuɗi N100 ne, VAT zai zama N7.50 kamar yadda bankin Zamani na Moniepoint ya aike da sakonni ga kwastamominsa.
Kamfanin Moniepoint ya ce wannan ba ƙarin farashi ba ne, wajibi ne na doka, kuma ana tura kuɗin kai tsaye zuwa Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS). Ya ƙara da cewa ribar ajiyar kuɗi a asusu ba ta cikin harajin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, matakin na daga cikin shirin gwamnati na daidaita karɓar VAT a harkokin kuɗin dijital da kuma ƙara samun kuɗaɗen shiga, yayin da aka tabbatar wa kwastomomi cewa harajin na VAT za a rika nuna shi a fili a bayanan mu’amala.



