Jam’iyyun ADC, PDP, NNPP da Labour Party sun soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan rahoton amincewa da kwangilar dala miliyan 9 domin yin toshiyar baki a Amurka, suna cewa gwamnati na ƙoƙarin goge hoton Nijeriya a waje alhali jama’a na fama da matsanancin tsaro da wahalar rayuwa.
ADC ta ce kuɗin ya nuna fifiko mara kyau, inda ta jaddada cewa babu wata toshiyar baki da zai ɓoye zubar da jini ko gazawar kare rayuka.
PDP ta ce inganta walwalar ’yan ƙasa ne kaɗai zai gyara hoton ƙasa, ba kwaɓaɓɓen toshin baki ba. NNPP kuma ta bayyana kwangilar a matsayin ɓarna, tana cewa tura jakadu zai fi dacewa wajen sadarwa da ƙasashen waje.
Rahotanni sun ce an ɗauki kamfanin DCI Group ta hannun Aster Legal a madadin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, domin bayyana ƙoƙarin gwamnati kan kare Kiristoci a Amurka.
Sai dai jam’iyyun adawa sun ce kashe irin wannan kuɗi a lokacin da talakawa ke fama da tsaro da tsadar rayuwa ya sabawa hankali, kuma ba zai maye gurbin sahihin tsarin kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya ba.



